Isa ga babban shafi
Najeriya

Kano: 'Yan Sanda sun kame dan majalisar tarayya tare da wasu 26

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama dan majalisar wakilai da ke wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, AbdulMumin Jibril, shugaban karamar hukumar ta Bebeji da kuma wasu mutane 26, bisa zarginsu da hannu a harin da aka kaiwa magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

AbdulMumin Jibril, da ke wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a majalisar wakilan Najeriya.,
AbdulMumin Jibril, da ke wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a majalisar wakilan Najeriya., Daily Post Nigeria
Talla

Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis 21 ga watan Fabarairu, inda wasu gungun matasa da ake zargin magoya bayan jam’iyyar APC ne masu biyayya ga dan majalisa AbdulMumin Jibril, suka afkawa tawagar yakin neman zaben Kwankwasiyya a kauyen Kofa da ke karamar hukumar ta Bebeji.

Tashin hankalin yayi sanadin mutuwar mutane 2, tare da kone motoci sama da 40, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar a yau Juma’a.

DSP Haruna, ya kara da cewa kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Muhammed Wakili, da kansa ya jagoranci sauran jami’ai zuwa inda tashin hankalin ya auku, ya kuma bada umarnin kama dan majalisar wakilan AbdulMumin Jibril.

Dan majalisar dai na cikin ‘yan takarar zaben ‘yan majalisun wakilan tarayyar Najeriya na bana, wadanda ke neman wakilcin kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.