Bakonmu a Yau
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Muhammad Kerewa, Ardon Zuru kan kisan da aka yiwa Fulani a karamar hukumar Kajuru ta Kaduna
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:43
Kungiyra Fulani ta Miyattai Allah da ke Najeriya ta gargadi yayan ta da su kaucewa daukar fansa kan kisan gillar da aka yi a karamar hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna, inda suka bukaci barin jami’an tsaro da gwamnati yin aikin da ya rataya a wuyan su.Shugaban kungiyar na kasa Muhammad Kerewa, Ardon Zuru yace sun gamsu da matakan da gwamnati dajami’an tsaro suka dauka ya zuwa yanzu.Ga dai abinda yake cewa a tattaunawar da muka yi da shi.