Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iyyun Najeriya za su ci gaba da yakin neman zabe- INEC

Hukumar Zaben Najeriya Mai Zaman Kanta, INEC ta bai wa jam’iyyun siyasa damar ci gaba da yakin neman zabe har zuwa karfe 12 na daren ranar Alhamis mai zuwa, bayan da farko hukumar ta ce, ba za a sake bai wa ‘yan siyasa wannan damar ba duk da cewa, an dage zaben da ya kamata a yi a karshen makon jiya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu News Express Nigeria
Talla

A yanzu dai INEC ta bai wa ‘yan siyasar damar shirya tarukan gangami da kuma aikewa da sakwanni ta kafafen yada labarai zuwa ga magoya bayansu, wannan kuwa bayan wata ganawa da aka yi tsakanin hukumar zaben da kuma wakilan jam’iyyun siyasar ne.

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya ce, zai umarci shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya yi wa al’ummar Najeriya bayani bisa matakinsa na dage zaben, al’amarin da ya haifar da rudanin siyasa a fadin kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, ya dace jama’a su san musabbabin dage zaben da kuma wadanda suka yi uwa da makarbiya wajen dage zaben na ranar 16 ga watan Fabairu.

Koda yake Hukunmar INEC ta ce, matsalar rashin isar da kayayyakin aiki a wasu wuraren, ita ce ta haddasa dage zaben na shuganban kasa da na ‘yan majalisu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.