Isa ga babban shafi
Najeriya

Martanin Buhari kan matakin dage zabukan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana rashin jin dadinsa matuka dangane da dage ranar gudanar da zabukan kasar na shugaban kasa da na ‘yan majalisun wakilai da kuma na dattijai.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. AFP
Talla

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta baiwa hukumar zaben Najeriya dukkanin taimakon da take bukata wajen gudanar da ayyukanta cikin nasara, amma sa’o’i kalilan suka rage a soma kada kuri’a, hukumar ta bayyana matakin sauya lokutan zaben, bayan da tuni ‘yan Najeriya suka yi amfani da lokacinsu wajen yin tafiye-tafiye zuwa gida, zalika wakilan masu sa ido kan zabukan a ciki da wajen Najeriya sun kammala hallara a kasar.

Buhari ya bayyana haka ne, cikin wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannunsa a Daura da ke jihar Katsina, inda ya ce dole hukumar INEC ta tabbatar da kare kayayyakin muhiman aikin zaben da ta tanada.

Shugaban Najeriyar, ya kuma bayyana cewa zai koma Abuja, domin tabbatar da nasarar taron da hukumar zabe za ta yi da dukkanin masu ruwa da tsaki, kan manyan zabukan Najeriyar na 2019.

A karshe shugaba Buhari, ya bukaci ‘yan Najeriya su guji aikata abubuwan da za su iya haddasa rikici, zalika su kansance masu karfafa kishin kasa da son juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.