Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya za su fayyace makomar shugaban kasa

Sama da ‘yan Najeriya miliyan 84 ake sa ran za su kada kuri’unsu domin fayyace makomar shugaban kasa a zaben 2019 da za a gudanar a gobe Asabar, yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, ta ce, ta kammala dukkanin shirye-shirye.

Sama da 'Yan Najeriya miliyan  84 ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben shugabancin kasar a ranar Asabar
Sama da 'Yan Najeriya miliyan 84 ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben shugabancin kasar a ranar Asabar thisdaylive.com
Talla

Tuni jam’iyyun siyasa suka kammala yakin neman zabensu a hukumance a ranar Alhamis bayan sun karade sassan kasar da zummar zawarcin kuri’un al’umma.

Sai dai a yayin gudanar da tarukan gangamin siyasar, an samu hatsaniya a wasu wurare da dama, in da a baya-bayan nan magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu, wato APC da PDP suka yi mummunan artabu da juna a jihar Adamawa, in da suka yi ta sassara junanasu da adduna.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoto kan artabun magoya bayan APC da PPD a Adamawa.

01:30

Artabun APC da PDP a Adamawa

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan takarar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya domin kauce wa tashin hankali a lokacin gudanar da zaben.

Rundunar ‘Yan sandan kasar ta ce, ta tanadi matakan tsaro tare da hana zirga-zirgar motoci a yayin gudanar da zaben, yayin da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar.

Hankula za su fi karkata ne kan manyan ‘yan takara wato, shugaba Muhammadu Buhari na APC mai mulki da kuma Atiku Abubakar na PDP mai adawa.

A bangare guda, masu sanya ido daga kasashen ketare sun isa Najeriya don ganin yadda zaben zai gudana.

A yayin zantarwarsa da RFI, Christopher Fomunyoh, Darektan Cibiyar Bunkasa Demokradiya ta NDI, reshen Afrika, ya ce, suna tare da ayarin ‘yan kallo su 40 daga kasashe 20 da suka hada da Afirka da Amurka da Turai da kuma Latin Amurka.

Fumunyoh ya ce, sun gana da wakilan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula, da hukumar zabe da ma sauran jami’ai domin sanin irin matakan da aka dauka wajen shirya wannan zabe, abin da ya ce, ya ba su damar kara fadakar da jami’ansu wadanda tuni aka rarraba su a sassa daban daban don sa ido a wannan zabe na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.