Jam’iyyar APC mai mulki za ta kammala yakin neman zabenta a jihar Katsina a yau Alhamis bayan ta gudanar da gangaminta a jiya a birnin Abuja, koda yake shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole da madugun jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba su samu damar halartar gangamin ba.
Ana rade-radin cewa, PDP za ta gudanar da nata gangamin wani lokaci a yau a birnin Abuja, amma babu wata kwakkwarar majiya daga bangaren jam’yyar da ta tabbatar da labarin.
Tun a jiya aka zaci cewa, PDPn za ta yi gangamin nata a Abuja, amma ya ci karo da na APC mai mulkin kasar.
A ranar Asabar mai zuwa ne, ake saran kimanin mutane miliyan 84 za su halarci rumfunan zabe a sassan kasar domin kada kuri’unsu ga wanda suke fatan kasancewa shugaban Najeriya a shekarar 2019.