Bakonmu a Yau
Farfesa Jibrin Ibrahim kan kalaman batanci a lokacin zabe
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:38
Yayin da ake shirin gudanar da zabukan Najeriya daga wannan mako, yanzu haka wata matsala da ta fito fili ita ce, yadda wasu 'yan siyasa ke furta kalaman batanci ko kuma tinzira jama’a domin tayar da tarzoma. Irin wannan matsalar ta haifar da tashin hankali a kasashe da dama da ke nahiyar Afirka. Akan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Farfesa Jibrin Ibrahim na Cibiyar Bunkasa Dimokiradiya a Najeriya.