Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta kara wa'adin karbar katunan zabe

Hukumar shirya zaben Najeriya INEC, ta kara wa'adin ci gaba da karbar katunan zabe na din-din-din da tsawon kwanaki uku.

Katunan zaben din-din-din na Najeriya.
Katunan zaben din-din-din na Najeriya. Sahara Reporters
Talla

Ranar Juma'a 8 ga watan Fabarairu, hukumar zaben ta tsara kawo karshen raba katunan, wanda a yanzu tace za a ci gaba da rabawa zuwa ranar Litinin, 11 ga watan Fabarairu.

Shugaban hukumar zaben ta Najeriya Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce matakin kara wa'adin, ya biyo bayan koken da jama'a da dama suka gabatar kan bukatar.

Farfesa Yakubu ya kuma ce, ma’aikatan hukumar ta INEC za su gudanar da aikin raba katunan zaben na din-din-din daga karfe 9 na safe, zuwa 6 na yamma a ranakun Asabar da Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.