Isa ga babban shafi
Najeriya

2019: Amurka ta gargadi 'yan siyasar Najeriya kan haifar da rikici

Amurka ta gargadi ‘yan siyasar Najeriya da cewa za su fuskanci tsattsauran hukuncinta, muddin kalamansu suka tunzura jama'a wajen tayar da rikicin da ya hana gudanar zabukan kasar dake tafe cikin kwanciyar hankali.

Jakadan Amurka a Najeriya Staurt Symington.
Jakadan Amurka a Najeriya Staurt Symington. YouTube
Talla

Jakadan Amurka a Najeriya Staurt Symington ne ya isar da sakon gargadin agarin Makurdi, bayan ganawa da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.

Symington ya bukaci ‘yan Najeriya da su gujewa yaudarar bata garin ‘yan siyasa, da ka iya yin amfani da sunan shugaban kasar Muhd Buhari wajen basu umarnin tada zaune tsaye.

Gargadin jakadan Amurkan ya zo ne kwanaki kadan, bayan da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufaí a kafar talabijin ta NTA, ya yi barazanar cewa, jami’an tsaron Najeriya, za su hallaka dukkanin wani dan kasar ketare da ya yi yunkurin katsalandan cikin al’amuran zaben kasar.

Tuni dai Kungiyar tarayyar Turai Eu ta maida martani kan kalaman na gwamnan Kaduna, inda ta ce jamiánta sun zo Najeriya ne sakamakon gayyatarsu da aka yi, kuma za su saído ne kawai, kan zaben kasar, ba wai katsalandan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.