Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/08 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/08 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/08 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 16/08 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/08 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/08 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

"Babu hannunmu wajen shigar da karar Buhari a kotu"

media Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sanatocin Jam'iyyar APC mai mulki Premium Times/Callistus /HB/NAN

Gungun Sanatocin Jam’iyyar APC da ke Majalisar Dattawan Najeriya ya nesanta kansa da matakin da Majalisar ta dauka na maka shugaba Muhammadu Buhari a kotu saboda dakatar da alkalin alkalan kasar, Walter Onnoghen.

Wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya sanya wa hannu, ta ce, babu hannun sanatocin na APC wajen daukan matakin shigar da karar Buhari a kotun.

Gungun na APC ya sanar da matsayarsa ne ga al’ummar Najeriya bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

Mai taimaka wa shugaban Majalisar, Bukola Saraki ta fannin yada labara, Yusuph Olaniyonu ya fitar da wata sanarwa da ke cewa , Majalisar ta shigar da kara a kotun kolin kasar domin neman sanin halascin dakatarwar da Buhari ya yi wa Onnoghen.

Shugaba Buhari ya dakatar da Onnoghen ne a ranar Juma’ar da ta gabata saboda zargin sa da bayar da bayanan karya kan kudaden da ya mallaka a asusunsa, abin da ya saba wa dokokin da kotun kula da da’ar ma’aikata ta kasar ta tanadar.

Sai dai ‘yan Najeriya da dama da suka hada da Kungiyar Lauyoyi, NBA na adawa da matakin dakatar da Onnoghen, in da suke cewa, shugaba Buhari ba shi da hurumin daukan irin wannan hukuncin a hannunsa.

Tuni NBA ta bukaci kotuna da su kaurace wa zama a ranakun Talata da Laraba a dukkanin fadin Najeriya domin zanga-zangar adawa da matakin.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure