Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yarda cewa an samu koma-baya a yaki da Boko Haram

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince cewa ana samun koma-baya a fafutukar kakkabe mayakan Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Audu MARTE / AFP
Talla

A yayin wata hirarsa da aka watsa ta kafar talabijin ta Arise a cikin daren da ya gabata, shugaba Buhari ya amince cewa, sojojin kasar na fuskantar matsin lamba daga mayakan na Boko Haram da ke amfani da salon yakin sunkuru.

Shugaban ya kuma amince cewa, sojojin kasar na fama da matsalar rashin karfafa musu guiwa a fagen-daga, amma ya ce, suna kan kokarin shawo kan wannan matsalar.

“ Akwai abin da zan kira gajiyawar yaki” in jin Buhari wanda ya kara da cewa, sake bai wa sojojin horo zai magance dabarun mayakan masu ikirarin jihadi.

Sojojin da ke fagen-daga sun sha korafi kan cewa, mayakan na Boko Haram sun mallaki makaman da suka zarce nasu, kuma ba sa samun kwarin guiwa yadda ya kamata a cewarsu.

A bangare guda, shugaban na Najeriya ya ce, yana nazari kan korafin rashin sallamar manyan hafsoshin tsaronsa bayan tsanantar hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.