Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai fara yakin neman zabe a Akwa Ibom

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai kaddamar da yakin neman zabensa wa’adi na biyu a ranar Juma’a mai zuwa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na neman wa'adi na biyu kan karagar mulki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na neman wa'adi na biyu kan karagar mulki premiumtimes
Talla

Sanata Ita Enang da ke taimaka wa Buhari kan al’amuran da suka shafi Majalisar Tarayya ya sanar da haka a yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin a Uyo.

Enang ya ce, shugaba Buhari zai kasance a jihar tare da shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Adam Oshiomhole da sauran jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar don kaddamar da yakin neman zaben a hukumance.

Sanatan ya ce, jam’iyyar APC ta nemi izinin amfani da katafaren filin wasan kasa da kasa na Akpabio kuma tuni gwamnatin jihar ta amince a cewarsa.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar, NAN ta ce, a ranar 23 ga watan Disamba, gwamnatin jihar ta ce, ba za ta bayar da filin don gudanar da yakin neman zaben ba saboda wasannin firimiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.