Isa ga babban shafi
Amurka-Najeriya

Cibiyar American Centre for Law and Justice ta bayar da labari da kuskure

Wani faifan bidiyo da lauyoyin shugaban Amurka Donald Trump suka sanya shafin dandalin sada zumuntar facebook yace makiyaya musulmi sun kashe kriistoci 60,000 a tsakiyar Najeria.

Wasu makiyaya a tsakiyar Daji
Wasu makiyaya a tsakiyar Daji Getty Images/Michael Fay
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya gudanar da bincike a kai, kuma bincike kan zargin da lauyan shugaba Donald Trump Jay Sekulow yayi a bidiyon da aka wallafa a facebook ranar 23 ga watan Nuwamba, cewar kabilar Fulani Musulmi ta kashe kristoci manoma 60,000, inda ya gano cewar ba haka lamarin yake ba.

Shidai faifan bidiyon ya samo assali ne daga wata Cibiyar tabbatar da shari’a da ake kira ‘American Centre for Law and Justice’ ta kiristoci dake Washington.

Binciken na kamfanin dillancin labaran Faransa domin tabbatar da gaskiyar labarin, ya gano cewar ba haka labarin yake ba, saboda babu wata shaida ta hakika dake tabbatar da haka, duk da yake an samu tashe tashen hankula daban daban.

Kamfanin dillancin labaran yace babu wani adadin mamata da aka dangata da wani addini, kuma babu wasu alkaluman mamata a rikice rikicen da aka samu da ya bada adadin da ya kai 60,000.

Kamfanin dillancin labaran yace yan ra’ayin rikau a Amurka na amfani da wannan rahoto domin cimma manufar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.