Isa ga babban shafi
Najeriya

An zargi 'Yan Jaridun Najeriya da fifita siyasa fiye da komai

An zargi ‘yan Jaridun Najeriya da mayar da hankali kan labarun siyasa maimakon janyo hankalin gwamnati da jama’a wajen ayyukan raya kasa da kuma haifar da cigaban al’umma.

Wasu 'yan jaridun Najeriya zagaye da wani dan siyasa yayin neman ra'ayinsa kan zaben kujerar gwamnan jihar Osun. 9/08/2014.
Wasu 'yan jaridun Najeriya zagaye da wani dan siyasa yayin neman ra'ayinsa kan zaben kujerar gwamnan jihar Osun. 9/08/2014. Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

Wata kungiyar ci gaba da ta duniya da ake kira Rebooth ta shirya taro na musamman ya janyo manema labarai da kuma 'Yan Jaridu domin tunatar da su kan nauyin da ya rataya akan su.

Wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi yayin taron sun kalubalanci 'Yan Jaridu da su rika mayar da hankali kan fannonin ci gaban al'umma kamar sha'anin wutar lantarki, da sauran batutuwan tattalin arziki, a maimakon maida hankali kan siyasa fiye da komai.

Wakilinmu daga Abuja, Muhammad Sani Abubakar ya aiko da rahoto akan taron.

01:31

An zargi 'Yan Jaridu da fifita sha'anin siyasa fiye da komai

Mohammed Sani Abubakar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.