Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Zamfara ta tsige masu rike da Sarautun Gargajiya 4

Gwamnatin Jihar Zamfara dake Najeriya ta sanar tube wasu masu rike da Sarautun Gargajiya 4 daga mukaman su, saboda zargin da ake musu na hada baki da masu aikata laifufuka ana cutar jama’a.

Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari. TheCable
Talla

Kwamishinan kananan hukumomi ya tabbatar da haka, inda yace daya daga cikin wadanda ake zargi yayi batan dabo, kuma ana cigaba da neman sa.

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamafar kuma Sarkin Zamfarar Anka Alh Attahiru Ahmad, ya shaidawa Sashin Hausa na RFI cewa koda yake dukkanin dan adam Ajizi ne, zai yi wahala wadanda suka gaji sarauta su aikata laifin hada baki da masu aikata manyan laifuka wajen cutar da talakawansu.

01:02

Muryar Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamafar kuma Sarkin Zamfarar Anka Alh Attahiru Ahmad

Bashir Ibrahim Idris

A karshen watan Nuwamban da ya gabata ne Gwamnatin Zamfara ta dakatar da wasu masu rike da sarautar gargajiya guda 4 da ake zargin cewar suna alaka da ‘Yan bindigar dake kashe jama’ar Jihar.

Yayin bayyana matakin a waccan lokaci, kwamishinan kula da kananan hukumomi da masarautu, Bello Dankande ya ce sarakunan sun hada da Hakimin Gora da ke Talatar-Mafara da Hakimin Barikin Daji, sai kuma Mai garin Gyado da Tungan Dutsi da ke karamar hukumar Bukkuyum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.