Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta musanta zargin dauko hayar magoya baya daga Nijar

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta musanta zargin da ake yi mata na dauko hayar dubban mutane daga Jamhuriyar Nijar, domin halartar taron kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasar dan takararta Atiku Abubakar ranar Litinin a Jihar Sokoto.

Taron jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Sokoto, yayin kaddamar da yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na dan takararta Atiku Abubakar.
Taron jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Sokoto, yayin kaddamar da yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na dan takararta Atiku Abubakar. TheCable
Talla

Martanin na PDP ya biyo bayan zarginta da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i, yayi na cewa ta dauko hayar mutanen daga Nijar ne domin nuna cewa tana da tarin magoya fiye da tunani.

A cewar el-Rufa’i jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa madafar da za ta dogara da ita wajen jan hankalin ‘yan Najeriya shi yasa ta dauko hayar mutane da sunan magoya baya.

Sai dai yayin da yake maida martani kan kalaman na Gwamnan Kaduna, Sakataren yada labaran PDP Mista Kola Ologbondiyan ya ce abin takaici ne a ce gwamnan yana korewa asalin ‘yan Najeriya da suka fito domin nuna musu goyon baya.

A cewar Mista Ologbondiyan, kalaman Gwamnan na jihar Kaduna, na nuni da cewa jam’iyya mai mulki ta APC ce, ke shirin dauko hayar mutane daga Chadi, Nijar da kuma Kamaru domin tafka magudi a zabukan shekarar 2019 mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.