Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kone gonakin shinkafa a Borno

Mayakan Boko Haram sun kone wasu gonakin shinkafa a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar Borno, lamarin da ya haddasa tafka hasarar daruruwan buhunan shinkafa da aka noma a daminar bana.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira mata da yara da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin kokarin diban ruwa a sansaninsu na Muna dake Maiduguri. 1/12/2016.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira mata da yara da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin kokarin diban ruwa a sansaninsu na Muna dake Maiduguri. 1/12/2016. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Malam Hassan Zabarmari shi ne shugaban manoman da matsalar ta shafa, wanda ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa yawan hasarar da suka yi ta wuce matakin kayyadewa sai dai kawai su kiyasta.

A cewar Hassan Zabarmari mayakan na Boko Haram sun kone sama da kadada ko fadin kasar da ya zarce eka 250 na gonaki.

Shugaban manoman ya ce akwai bukatar gwamnati ta gaggauta kawo musu dauki la’akari da halin kuncin da harin kone musu gonakin ya jefa su.

00:35

Muryar Malam Hassan Zabarmari shugaban manoman da 'yan Boko Haram suka konewa gonaki

Nura Ado Suleiman

A karshen watan Nuwamba mayakan Boko Haram kai hari kan wasu gonaki inda suka kashe manoma guda 4 a kauyen Ali Gamarguri lokacin da suka same su suna aiki.

Harin dai ba shi ne na farko da mayakan Boko Haram ke kaiwa manoma ba, kasancewar a tsakiyar watan na Nuwamba, sun hallaka manoma 9 tare da sace wasu 12 daga kauyen Mammanti dake gaf da birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.