Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 28/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 28/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 28/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kone gonakin shinkafa a Borno

media Wasu daga cikin 'yan gudun hijira mata da yara da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin kokarin diban ruwa a sansaninsu na Muna dake Maiduguri. 1/12/2016. REUTERS/Afolabi Sotunde

Mayakan Boko Haram sun kone wasu gonakin shinkafa a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar Borno, lamarin da ya haddasa tafka hasarar daruruwan buhunan shinkafa da aka noma a daminar bana.

Malam Hassan Zabarmari shi ne shugaban manoman da matsalar ta shafa, wanda ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa yawan hasarar da suka yi ta wuce matakin kayyadewa sai dai kawai su kiyasta.

A cewar Hassan Zabarmari mayakan na Boko Haram sun kone sama da kadada ko fadin kasar da ya zarce eka 250 na gonaki.

Shugaban manoman ya ce akwai bukatar gwamnati ta gaggauta kawo musu dauki la’akari da halin kuncin da harin kone musu gonakin ya jefa su.

Muryar Malam Hassan Zabarmari shugaban manoman da 'yan Boko Haram suka konewa gonaki 04/12/2018 - Daga Nura Ado Suleiman Saurare

A karshen watan Nuwamba mayakan Boko Haram kai hari kan wasu gonaki inda suka kashe manoma guda 4 a kauyen Ali Gamarguri lokacin da suka same su suna aiki.

Harin dai ba shi ne na farko da mayakan Boko Haram ke kaiwa manoma ba, kasancewar a tsakiyar watan na Nuwamba, sun hallaka manoma 9 tare da sace wasu 12 daga kauyen Mammanti dake gaf da birnin Maiduguri.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure