Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun dakile harin mayakan Boko Haram a Arege

Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya sun shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP a jiya Juma’a cewa, mayakan Boko Haram sun hallaka jami’insu guda a wani hari da suka kai kan sansaninsu a kauyen Arege dake gaf da garin Baga.

Wasu sojin Najeriya a kauyen Hausari yayin gudanar da sintiri. 05/06/2013.
Wasu sojin Najeriya a kauyen Hausari yayin gudanar da sintiri. 05/06/2013. REUTERS/Joe Brock
Talla

Majiyar tace mayakan sun zo ne akan motoci masu dauke da manyan bindigogi a gaf da wayewar ranar ta Juma’a, to sai dai bayan musayar wuta, sojin Najeriyar sun yi nasarar tarwatsa gungun mayakan.

Bayaga soja guda da ya rasa ransa wasu akalla guda 7 sun jikkata a fafatawar.

Harin baya bayan nan ya zoo ne kwana guda bayanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Chadi, inda ya gana da shugaban kasar da sauran takwarorinsu na Nijar da Kamaru dangane da daukar matakan kawo karshen sabbin hare-haren da mayakan na Boko Haram suke kaiwa akai-akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.