Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun hallaka manoma 4

Rahotanni daga Jihar Borno a Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun kashe wasu manoma guda 4 a kauyen Ali Gamarguri lokacin da suka same su suna aiki a gonakin su.

Wani tsohon hoton jagoran mayakan Boko haram Abubakar Shekau.
Wani tsohon hoton jagoran mayakan Boko haram Abubakar Shekau. © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wani shaidar gani da ido da ya tsallake rijiya da baya, Abba Muhammed ya shaidawa wakilinmu Bilyaminu Yusuf cewa yana tare da Mahaifinsa da kuma matarsa ne a lokacin mayakan na Boko Haram suka iske su a gona.

A cewar Abba Muhammed dukkanin manoman 4 da mayakan suka hallaka yankan rago aka yi musu yayinda suka jikkata wasu manoman 2 ta hanyar sassara su.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da mayakan Boko Haram ke kaiwa manoma hari ba, kasancewar a makon da ya gabata, sun hallaka manoma 9 tare da sace wasu 12 daga kauyen Mammanti dake gaf da birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.