Isa ga babban shafi
Najeriya

APC za ta kalubalanci INEC a kotu kan jihar Zamfara

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Kwamrade Adams Oshiomhole, ya sanar da baiwa lauyoyin jam’iyyar umarnin garzayawa kotu, domin kalubalantar matakin da hukumar zaben kasar INEC ta dauka, na haramtawa jam’iyyar ta APC gabatar da ‘yan takararta a jihar Zamfara yayin zabukan 2019.

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomhole.
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomhole. Daily Post
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a karshen mako, Oshiomhole ya ce hukumar INEC ba ta da hurumin daukar matakin, wanda yace tamkar ta  takaitawa al’ummar jihar Zamfara damar zabinsu ne yayin zabukan na 2019, matakin da ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar cewa kotu za ta yi adalci wajen soke shi.

A ranar 10 ga watan Oktoban da ya gabata, INEC ta ce, jam’iyyar APC mai mulki ba ta da damar tsaida dan takara a dukkanin matakan zabukan Zamfara a 2019, saboda gazawarta wajen kammala gudanar da zabukan fidda ‘gwani a jihar, cikin wa’adin da hukumar ta INEC ta debawa daukacin jam’iyyun siyasar Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.