Isa ga babban shafi
Najeriya

WAEC ta mikawa Buhari sakamakonsa

Hukumar dake shirya jarrabawar kammala makarantar Sakandare ta yammacin nahiyar Afrika, WAEC, ta gabatarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shaidar sakamakonsa na rubuta jarrabawar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin karbar shaidar sakamakonsa na Jarrabawar kammala makarantar Sakandare WAEC, daga magatakardar hukumar Dakta Iyi Uwadiae.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin karbar shaidar sakamakonsa na Jarrabawar kammala makarantar Sakandare WAEC, daga magatakardar hukumar Dakta Iyi Uwadiae. RFIHAUSA
Talla

Mataimakin shugaban na musamman akan kafafen yada labarai, Femi Adeshina ne ya bayyana a wannan Juma’a haka a shafinsa na Twitter.

Dakta Iyi Uwadiae, magatakardan hukumar shirya jarrabawar ta WAEC, ya gabatarwa da shugaba Buhari shaidar sakamakonsa a fadar gwamnati dake Abuja, inda manyan jami’an shugaban suka samu halarta, ciki harda Ministan Ilimi Adamu Adamu.

Kafin daukar wannan da hukumar WAEC ta yi, an shafe tsawon lokaci ana ce-ce-ku-ce akan ko shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na da shaidar Jarrabawar, inda jam’iyyun adawar kasar ke matsin lamba ga shugaban da jam’iyyarsa kan lamarin.

An samu tafka muhawara kan batun shaidar rubuta jarrabawarce a baya bayan nan, a lokacinda shugab Buhari ya shaidawa hukumar zaben Najeriya INEC cewa, har yanzu sakamakonsa yana hannun rundunar sojin kasar.

A dalilin hakan, a ranar 26 ga watan Oktoba, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaban da ya tabbatar da cancantarsa, ta hanyar gabatarwa da hukumar INEC sakamakon rubuta jarrabawar kammala sakandaren ta WAEC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.