Isa ga babban shafi
Najeriya

Wa'adin INEC ga jam'iyyu kan mika sunayen 'yan takara ya kare

A wanna Juma'a 2 ga watan Nuwamba 2018, wa'adin da hukumar zaben Najeriya ta dibawa jam'iyyun siyasar kasar na mika mata sunayen 'yan takarar da zasu tsaida a zaben 2019 mai zuwa ya cika.A cewar hukumar zaben, Jam'iyu 79 ne dai daga cikin jam'iyu 89 suka fitar da wadanda zasu yi musu takarar kujerar Shugaban kasa, yayin da 'yan takarar 1,803 suke neman kujerun majalisar Dattawa 109. Haka kuma akwai mutane 4,548 da ke neman tsayawa takarar kujerun majalisar wakilai 360.Sai dai ga dukkan alamu rikici na neman dabaibaye jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, tsakanin shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole, da kuma wasu gwamnonin jam’iyyar, lamarin da ake ganin na iya shafar jamiyar gaba daya.Daga Abuja wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya aiko mana da wannan rahoton.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu daga tsakiya.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu daga tsakiya. Ventures Africa
Talla
03:01

Wa'adin INEC ga jam'iyyu kan mika sunayen 'yan takara ya kare

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.