Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun kama mutane 32 a Kaduna

Jami’an tsaro a Kaduna sun kama akalla mutane 32, bisa zarginsu da hannu wajen sake haddasa tashin hankalin da ya haifar da zaman dar-dar a cikin gari da wasu sassan jihar.

Wasu jami'an 'yan sanda yayin gudanar da aikin sintiri a arewacin jihar Kaduna. (04/10/2018).
Wasu jami'an 'yan sanda yayin gudanar da aikin sintiri a arewacin jihar Kaduna. (04/10/2018). REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Cikin sanawar da ya fitar a wannan Asabar, kakakin gwamnatin Kaduna Samuel Aruwan, ya ce yayinda dokar hana fita ke cigaba da aiki a jihar, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile yunkurin da wasu suka yi na kone wuraren Ibada a unguwannin hayin Banki da Kawo.

Aruwan ya kuma tabbatar da rahoton hallaka wani mutum guda a yankin Kasuwan magani, yayinda aka kama wani dauke da makami a lokacinda yake yunkurin kone kasuwar yankin.

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta Kaduna ta sanar sassauta dokar hana fita a karamar hukumar Kachia, inda a yanzu zirga-zirgar ta takaita daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yammaci.

Sake kakaba dokar hana fita da gwamnatin Kaduna ta yi a Juma’ar nan da ta gabata, ya biyo bayan zaman dar-dar da jama’a suka sake fuuskanta, bayan gano gawar Sarkin Kadara, mai rike da sarautar Agom Adara, Maiwada Galadima, wanda aka sace a Juma’ar makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.