Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun yi barazanar sake shiga yajin aiki

Gamayyar kungiyoyin kwadago na Najeriya, da suka hada da NLC, TUC, da kuma ULC, sun yi gargadin tsunduma cikin yajin aikin gama gari daga ranar 6 ga watan Nuwamba, muddin gwamnati taki sauraron bukatunsu.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar tattakin 'ya'yan kungiyar kwadago a garin Abuja. (9/02/2017).
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar tattakin 'ya'yan kungiyar kwadago a garin Abuja. (9/02/2017). REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kungiyoyin kwadagon sun ce idan har gwamnonin jihohi da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya suka amincewa da karin yawan mafi karancin albashin ma’aikata, to fa basu da zabi illa sake tsunduma cikin yain aikin sai baba ta gani.

Cikin wata sanarwar da suka fitar, gamayyar kungiyoyin na NLC, TUC da kuma ULC sun yi Allah wadai da matakin gwamnatin Najeriya na shirin aiwatar da hukuncin kin biyan albashi ga wadanda suka shiga yajin aiki.

Idan za a iya tunawa, a karshen makon da ya gabata gwamnonin jihohi 36 na Najeriya suka ce basu da karfin tattalin arzikin biyan sabon tsarin mafi karancin albashi da gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar ke nema.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari ne ya bayyana matsayar tasu, sa’o’i bayan taron da suka yi a Abuja ranar Larabar da ta gabata, wanda suka gayyaci shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Wabba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Abdul Aziz Yari, yace dukkaninsu na goyon bayan kara yawan mafi karancin albashin ma’aikata a kasar, sai dai matsalar ita ce basu da isassun kudaden tabbatar da muradin.

Sai dai yayin taron da suka yi, gwamnonin sun cimma matsayar soma shirin tabbatar da cewa kowannensu ya biya ma’aikatan dake jiharsa basukan da suke bi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.