An kafa dokar hana zirga-zirga a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna da ke tarayya Najeriya ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24 domin tabbatar da doka da oda a ciki da wajen gari.
Wallafawa ranar:
Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da daukar matakin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Ladin nan.
Al’amarin rashin tsaron ya biyo bayan rikicin da aka samu a yankin Kasuwan Magani dake karamar hukumar Kajuru ranar Alhamis 18 ga Oktoba, inda akalla mutane 55 suka rasa rayukansu.
Wakilinmu daga Kaduna Aminu Sani Sado ya aiko mana da rahoto kan halin da ake ciki.
An kafa dokar hana zirga-zirga a Kaduna
A watan fabarairun da ya gabata an taba samun makamancin wannan rikici, a yankin na Kasuwan Magani, inda akalla mutane 10 suka mutu, daga bisani kuma aka kama wasu mutane 65 bisa zarginsu da hannu cikin rikicin, har yanzu kuma shari’ar da ake musu a kotu na ci gaba da gudana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu