Isa ga babban shafi
Najeriya

Red Cross na neman taimakon Najeriya kan Boko Haram

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta roki gwamnatin Najeriya da ta ceto ma’aikatanta na lafiya guda biyu da ke hannun Kungiyar Boko Haram, ganin wa’adin da kungiyar ta bayar na hallaka su na karatowa.

Boko Haram ta bada wa'adin kashe ma'aikatan Red Cross
Boko Haram ta bada wa'adin kashe ma'aikatan Red Cross News Ghana
Talla

Kungiyar ta ce, tana cikin damuwa kan halin da Hauwa Liman da Alice Loksha ke ciki, ganin yadda kungiyar ta kashe Saifura Khorsa kwanakin da suka wuce.

Shugaban gudanar da ayyukan Kungiyar, Mamadow Sow ya bukaci duk masu hannu cikin lamarin da su taimaka wajen kubutar da ma’aikatan da ransu.

Mai magana da yawun Red Cross a Najeriya, Alexandra Majetovic Minomsma  ta yi karin bayani game da sanarwarsu, in da ta ke cewa, "Mun gabatar da wannan sanarwar ce a matsayin wani yunkuri na rokon wadanda suka kama su, da suyi afuwa wajen sake su ba tare da sun jikkata su ba."

Jami'ar ta kara da cewa, "A matsayinmu na Kungiyar Agaji, ba ma biyan diyya kan ma’aikatanmu da aka kama koda kuwa yaya yanayin aikinsu yake, ko kuma kasar da suka fito. Ba ma ciniki akai, amma mun aike da sakwanni ta hanyoyi da dama domin rokon su da su gaggauta sakin wadannan mata.".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.