Isa ga babban shafi
Najeriya

Ganduje: Za mu dauki matakin shari'a kan Jaafar Jaafar

Jaridar Daily Nigerian ta Najeriya ta wallafa faifen bidiyon da ke nuna Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudade a matsayin cin hanci da yawansu ya kai Dala miliyan 5 a cewar Jaridar. Koda yake gwamnatin jihar ta ce, bidiyon na bogi ne kuma za ta shigar da kara a kotu.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Daily Post
Talla

Wani dan kwangila da ya bukaci a sakaya sunansa, shi ne ya yi amfani da biro da agogon hannu wajen nadan hotunan bidiyon da ke nuna Ganduje na soke Dalolin a aljihunsa, amma gwamnatin ta musanta wannan zargi.

Fallasa wannan bidiyo na zuwa ne bayan kwanakin da aka kwashe na yayata labarin zargin Gwamna Ganduje da karbar kudaden cin hanci daga ‘yan kwangila.

Jim kadaan da fitar da bidiyon mai tsawon minti 2 da dakikoki 27, RFI Hausa ta zanta da Jaafar Jaafar, mawallafi kuma Editan jaridar ta Daily Nigerian.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraron hira da Ja'afar Ja'afar da kuma martanin gwamnatin jihar Kano.

01:39

Hira da Ja'afar Ja'afar da kuma martanin gwamnatin Kano

Salihu Tanko Yakasai, mataimaki na musamma ga Ganduje kan harkokin yada labarai ya shaida wa RFI Hausa cewa, an wallafa bidiyon ne don bata sunan Gwamna kuma za su shigar da batun a kotu domin a cewarsa, kage aka yi wa Ganduje.

Bidiyon ya nuna  Ganduje na karbar rafa-rafa na Dala a zaune kan wata koriyar kujera kafin daga bisani ya mike tsaye, sannan kuma ga tutar Najeriya a bayansa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.