Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Zuru kan haramta wa mutane 50 fita daga Najeriya

Wallafawa ranar:

Matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na haramta wa mutane 50 fita daga kasar saboda zargin su da zargin su da cin hanci da rashawa ya haifar da cece-kuce. Wata sanarwar da Garba Shehu ya raba wa manema labarai dangane da matakin ta ce, shugaban ya sanya hannu kan dokar ce wadda ta shafi wadanda ake zargi da aikata manya-manyan laifukan da ke da nasaba da cin hanci da rashawa. Duk da yake gwamnati bata bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, amma Jaridar The Nation ta wallafa sunayen da suka hada da na tsoffin Gwamnoni 13 da tsoffin Mninistoci da tsoffin Hafsoshin Soji da Alkalai da kuam Lauyoyi. Wata Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta SERAP ta ce, dokar ta saba ka’ida kuma karen-tsaye ne ga 'yancin mutanen da abin ya shafa. Akan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari’a a Najeriya, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.