Isa ga babban shafi
Najeriya

APC da INEC na takaddama kan zaben Zamfara

Takaddama ta kunno kai tsakanin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da hukumar shirya zabukan kasar mai zaman kanta INEC, dangane da makomar jam’iyyar a zabukan jihar Zamfara.

Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara.
Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara. TheCable
Talla

Sabanin ya kunno kai ne, bayanda INEC ta ce APC ba ta ikon shiga duk wasu zabukan da za su gudana a jihar ta Zamfara, in dai ba na shugaban kasa ba.

INEC ta ce haramcin ya hau kan APC ne, saboda jam’iyyar ta gaza warware rikicin cikin gidan da ya kunno kai a zaben fidda gwanin jihar, lamarin da ya haifar da tsaikon bayyana dan takararta a zaben kujerar gwamna kan lokaci.

Sai dai cikin wata wasika da jam’iyyar APC ta aikewa INEC, ta jaddada cewa ‘yan takararta zasu fafata a dukkanin zabukan jihar ta Zamfara dake tafe a shekara mai kamawa, duk da cewa INEC ta ce yunkurin na APC ya sabawa kundin dokar zaben Najeriya na shekarar 2010, sashi na 87 da 21.

Uzurin da INEC ta bayyana dai bai karbu a wajen APC ba, wanda ta bayyana shi a matsayin marar tushe.

Jam’iyyar APC ta ce, takwararta jam’iyyar PDP mai adawa, bata gudanar da zaben fitar da gwaninta don zaben gwamna a Kano ba, kuma INEC bata aike mata da irin wasikar haramcin shiga zabuka a jihar ba.

Idan za’a iya tunawa dai hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta, ta gargadi jam’iyyun kasar da cewa, ba zata tsawaita ko kara musu wa’adin ranar 7 ga watan Oktoba da ta sanya a matsayin ranar karshe ta gudanar da zaben fidda gwanin ‘yan takara ba.

Rudanin da ya kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki reshen Zamfara, ya samo asali ne daga sabani tsakanin gwamnan jihar AbdulAziz Yari mai neman tikitin takarar sanata da kuma Sanata Kabiru Marafa dake neman tikitin kujerar gwamnan jihar.

Yayinda gwamna Yari ke goyon bayan kwamishinan kudi Mukhtar Idris, shi kuwa Sanata Kabiru Marafa mai neman jam’iyyar ta APC ta bashi tikitin takarar gwamnan, ya dage kan a bi tsarin gudanar da zaben fidda gwani cikin baiwa kowa ‘yanci.

Takaddamar ce ta kai ga cewa, an gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar kujerar gwamnan jihar ta Zamfara kashi biyu, hakan tasa kwamitin lura da harkokin jam’iyyar APC na kasa a karkashin jagorancin shugabanta Adams Oshoimhole ya rushe, shugabancin jam’iyyar na jihar, matakin da bai yiwa gwamna dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.