Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dakta El Harun Muhammad kan komawar majalisun dokokin Najeriya bakin aiki

Wallafawa ranar:

A ranar Talata, 9 ga watan Oktoba na 2018, majalisun dokokin Najeriya suka dawo bakin aiki, bayan shafe tsawon lokaci suna hutu. Daya daga cikin manyan al'amuran da suka dauki hankula a majalisun, shi ne taron da wasu sanatocin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya suka gudanar a cikin daren da ya gabata game da makomar shugaban Majalisar Dattawan Kasar, Bukola Saraki.Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta El Harun Muhammad na na Babbar Kwalejin Fasaha ta Kaduna kan makomar aikin majalisun dokokin Najeriyar, la'akari da bukatun 'yan Najeriya da kuma yanayin tafiyar da ayyukan majalisun.

Wasu 'yan majalisun dokokin Najeriya a babban birnin kasar Abuja. Hoto (10/10/2012)
Wasu 'yan majalisun dokokin Najeriya a babban birnin kasar Abuja. Hoto (10/10/2012) REUTERS/Afolabi Sotunde)
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.