Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP na taro a Fatakwal don zabo dan takararta a 2019

An soma tantance wakilan babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wadanda zasu kada kuri’a a zaben fidda gwanin, da zasu tsayar da dan takararsu, a zaben shugabancin kasar da za a yi a 2019.

Babban taron jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya a garain Fatakwal na jihar Rivers.
Babban taron jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya a garain Fatakwal na jihar Rivers. Daily Times Nigeria
Talla

Rahotanni daga garin Fatakwal dake karbar bakuncin taron cikin tsauraran matakan tsaro, sun ce an samu fitowar wakilan jam’iyyar masu yawa, wadanda zasu tantance gwanin da zasu tsaida.

Yayinda da ake cigaba da shirye-shiryen soma zaben fidda gwanin ne, tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar ta PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmad Makarfi ya musanta, rahotannin da wasu ke yadawa kan cewa ya janye kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin Najeriyar.

Wasu daga cikin ‘yan takara 13 dake neman jam’iyyar ta PDP ta tsaida su a zaben na 2019, sun hada da, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki, da tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.