Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 28/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 28/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 28/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 28/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 28/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 26/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 26/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Najeriya: Ambaliyar ruwan bana ka iya haifar da karancin shinkafa a 2019

media Wani manomin shinkafa yayin aiki a gonarsa dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. 2 ga Maris, 2017. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya, ta yi gargadin mai yiwuwa a fuskanci karancin wadatar shinkafa a sassan kasar, sakamakon gagarumar ambaliyar ruwan bana da ta aukawa akalla jihohi 14.

Yayin gargadin na ranar Alhamis a garin Abuja, ministan albarkatun noma da raya karkara na Najeriya, Audu Ogbeh, ya ce idan har ba’a yi gaggawar daukar matakin sake shuka shinkafar da ambaliyar ruwan bana ta lalata ba, za’a fuskanci karancinta a cikin shekarar 2019.

Ministan ya ce jihohin da ambaliyar bana tafi shafa, wadanda sune kan gaba wajen noman shinkafa a Najeriya, sun hada da Kebbi, Jigawa, Kogi da kuma Anambra.

Ogbeh ya ce domin daukar matakan rigakafi a nan gaba, kwararru a cibiyar bincike da inganta iri ta Najeriya, sun dukufa wajen samar da ingantaccen irin shinkafa na ‘Faro 66 da Faro 67’ wadanda suke jurewa fuskantar ambaliyar ruwa, domin baiwa manoman Najeriya su shuka a wadace.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure