Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iyyar APC ta goyi bayan sake takarar Buhari a 2019

Rahotanni daga jihohin tarayyar Najeriya sun ce, shugaban kasar Muhd Buhari, ya samu gagarumin goyon baya daga wakilai da sauran manbobin jam’iyyarsa mai mulki ta APC, a zaben fidda dan takarar shugabancin kasar a zaben 2019 da ya gudana a wannan Juma’a da ta gabata 28 ga Satumba, 2018.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Stringer
Talla

Rahotannin sun ce duk da cewa shugaba Buhari ne dan takarar jam’iyyar ta APC tilo da ya gabatar da bukatar neman a sake bashi dama, an samu fitowar ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki sosai.

A jihar Rivers an rawaito cewa kimanin ‘ya’ayn jam’iyyar ta APC dubu 388 suka goyi bayan sake takarar shugaban, yayinda jigawa kuma ya samu kuri’u kimanin dubu 202.

A nata bangaren, a dai wannan Juma’ar ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriyar ta cimma matsayin gudanar da nata zaben fidda gwanin da zai mata takarar shugabancin kasar a jihar Rivers.

Kafin yanke shawarar dai, rahotanni sun ce, an yi ta samun sabani, tsakanin wasu daga cikin jagororin jam’iyyar adawar, kan zabin inda yakamata a gudanar zaben fidda gwanin dan takararta, a zaben shugabancin Najeriyar.

Akalla ‘yan takara 13 ake sa ran zasu tsaya zaben fidda gwanin jam’iyyar ta PDP, daga ciki kuma kwai tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.