Isa ga babban shafi
Najeriya

An saki malaman kwalejin sha'anin kiwon lafiya da aka sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce an saki malaman kwalejin sha’anin kiwon lafiya dake Makarfi, wadanda wasu gungun mutane suka sace kwanaki biyu da suka gabata.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. Ventures Africa
Talla

Bayanai sun ce malaman da suka hada da mata biyu da namiji daya, na kan hanyarsu ta komawa Makarfi daga Zaria, a lokacin da aka yi awon gaba da su, a ranar 17 ga watan Satumba da muke ciki, inda gungun mutanen suka yasar da motar malaman a gaf da Tashar Yari.

Yayin da yake yiwa sashin Hausa na RFI karin bayani akan halin da ake ciki, Yakubu Sabo Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya ce sun samu shugabancin Kwalejin sha’anin kiwon lafiyar ya tabbatar musu da sakin malaman.

Sai dai a cewar kakakin rundunar 'yan sandan na Kaduna, a nasu bangaren, suna ci gaba da farautar gungun mutanen da suka sace malaman, inda ya nemi jama'a da su ci gaba da basu hadin kai wajen fallasa wadanda basu yadda da motsinsu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.