Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/08 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/08 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/08 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 16/08 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/08 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/08 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/08 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe shugabansu

media Abu Musab Al-Barnawy da ke jagorancin bangaren Mamman Nur Guardian Nigeria

Majiyoyi kwarara sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, mayakan Boko Haram sun kashe shugabansu da ke jagorancin wani bangare na kungiyar, Mamman Nur.

Majiyoyin da ke da cikakkiyar masaniya game da Boko Haram sun ce, wasu jiga-jigan makusantansa ne suka kashe shi a ranar 21 ga watan Agusta biyo bayan rashin gamsuwa da salon jagorancinsa, musammam ganin yadda yake da rauni idan aka kwatanta shi da Abubakar Shekau.

A shekarar 2014 ne, Mamman Nur ya jagoranci boren da mayakan suka yi wa shugabansu Abubakar Shekau har aka samu tsagin shugabancin Abu Mus’ab Al-Barnawy.

Koda dai wasu majiyoyin na cewa, Mamman Nur ne hakikanin shugaban tsagin na Al-Barnawy, kawai dai ya mika masa ragama ne saboda darajar mahaifinsa, Mohammed Yusuf da aka kashe a shekarar 2009.

sunan Al-Barnawy dai “Habib”, kuma mahaifinsa ne ya assasa kungiyar ta Boko Haram.

Kwo yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da mutuwar Nur ba wanda aka kashe matarsa a wani samame da rundunar ta kai maboyar kungiyar a yankin tafkin Chadi a cikin watan Janairu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure