Buhari ya nada sabon shugaban hukumar DSS
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tsaron Farin kaya DSS, in da ya maye gurbin Mathew Seiyefa da ke rike da mukamin a matsayin riko, biyo bayan tube Lawal Daura daga mukaminsa a farkon watan jiya.
Wallafawa ranar:
Yusuf Magaji Bichi, gogaggen jami’i ne a hukumar ta DSS sakamakon rike mukamai da dama a karkashinta, ciki har da shugabanci a matakai daban daban, baya ga horon da ya samu a ciki da wajen kasar kan dubarun tara bayanan sirri.
Bichi wanda tuni ya kama aiki a yau, 14 ga watan Satumba, ya halarci makarantar Sakandare ta Danbatta da ke Kano da Kwalejin Ilimi mai zurfi ta jihar kafin daga bisa ya kammala digirinsa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a fannin kimiyar siyasa.
Tuni wannan nadin ya haifar da cece-kuce a Najeriya, in da wasu daga yankin kudancin kasar ke cewa, ya dace a Mathew Seyeifa akan mukamin a maimakon 'yan arewa su mamaye daukacin shugabancin hukumomin tattara bayanan sirrin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu