Isa ga babban shafi
Najeriya

Ambaliyar ruwa ta ci kananan hukumomi 8 a Kano

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano a Najeriya ta ce, ta tura jami’anta zuwa wasu yankuna a kananan hukumomi takwas da ke jihar da suka gamu da ambaliyar ruwa don tantance irin girmar barnar da ibtila'in ya haifar.

Ambaliyar ruwa na haddasa asarar rayuka da dukiya da albarkantun gona
Ambaliyar ruwa na haddasa asarar rayuka da dukiya da albarkantun gona RFIHAUSA/Awwal
Talla

Babban Sakateren Hukumar, Alhaji Ali Bashir ya bayyana haka a yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN a ranar Alhamis.

Bashir ya ce, jami’an hukumar za su tattara bayanai game da halin da yankunan ke ciki bayan aukuwar ibtila’in a Rimin Gado da Tofa da Dawakin Tofa da Gwarzo da Danbatta da Kabo da Gezawa da kuma Gabasawa.

Babban Sakataren bai bada bayani ba kan adadin mutanen da lamarin ya shafa, amma ya ce, za su mika rahoton bincikensu ga gwamnatin jihar da zaran sun kammala tattara bayanai.

Jihohi da dama a Najeriya na fama da ambaliyar ruwa a baya-baya nan, lamarin da ke haddasa asarar dimbin dukiya da gidajeje da kuma albarkatun gona har ma da rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.