Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu ruwanmu da takaddamar neman tsige Saraki - Miyetti Allah

Kungiyar Miyetti Allah ta nesanta kanta daga kalaman siyasar da wani memba a cikinta ya furta inda ya nemi shugaban najalisar dattijan Najeriya ya sauka daga mukaminsa ko a tsige shi.

Wasu Fulani makiyaya a Najeriya.
Wasu Fulani makiyaya a Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Matakin na Miyetti Allah ya biyo bayan martanin da jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta maida inda ta bukaci gwamnatin kasar, ta bayar da umurnin kama shugabannin kungiyar ta Miyetti Allah a jihar Benue, bayan da Garius Gololo daya daga cikin jagororinta ya bukaci shugaban majalisar dattawa Bokula Saraki ya sauka daga mukaminsa ko kuma a tilasta masa yin hakan.

Tun a ranar Talata da ta gabata ne Gololo ya gargadi Saraki da ya gaggauta sauka daga mukamin nasa, wani batu da har yanzu ake tafka muhawara kansa a dandalin siyasar Najeriya, tun bayan da shugaban majalisar dattijan ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa PDP.

Yayin da take bayyana bacin rai kan al’amarin na baya bayan nan, jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa da akwai alaka tsakanin kungiyar ta makiyaya da kuma gwmanatin APC.

To sai dai a lokacin da muka tuntubi shugaban kungiyar ta Miyetti Allah reshen jihar Benue Ubbi Haruna ta wayar tarho, ya shaida mana cewa, wanda ake cewa ya furta kalamai, ba shi da alaka da shugabancin kungiyar ta su, ba shi kuma da hurumin yin magana da yawunta.

Ubbi Haruna ya ce duk da cewa Garius Galolo mamba ne a cikin kungiyar ta Miyetti Allah, babu alaka tsakanin kalaman na Gololo da da ita, zalika Miyetti Allah ba ta da alaka da siyasa.

01:00

Shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar Benue Ubbi Haruna

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.