Isa ga babban shafi
Najeriya

Ina nazari kan tsayawa takarar shugabancin Najeriya - Saraki

Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce yana nazari taka takara a zaben shugabancin kasar na 2019.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja. 8 ga Agusta, 2018
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja. 8 ga Agusta, 2018 REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Saraki ya bayyana aniyar tasa ce a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta ‘Bloomberg’ mai hedikwata a birnin New York, inda ya ce yana da kwarin gwiwar zai iya kawo kyakkyawan sauyi a al’amuran Najeriya.

Yayin da yake tsokaci akan datse kofar shiga majalisun kasar da jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi, Saraki ya ce kamata ya yi a ce ‘yan Najeriya sun damu matuka kan matakin, la’akari da cewa ba’a hakan bait aba faruwa a tarihin kasar ba.

Saraki ya kara da cewa, ba zai yi mamaki ba, idan har gwamnatin shugaba Buhari ta yi amfani da jami’an tsaro a zaben 2019, ganin cewa ‘yan Najeriya sun yanke kyakkyawan fatan da suke yiwa gwamnatin mai ci.

Shugaban majalisar dattijan ya ce a ra’ayinsa kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta maido da tallafin sauke farashin man fetur, ta hanyar ware wa tallafin kasafi na musamman, domin baiwa bangaren ‘yan kasuwa damar shiga sha’anin shigo da man fetur daga kasashen ketare.

A cewar Saraki, Najeriya tana bukatar jagorancin shugaban kasa mai ra’ayin ciyar da fannin cinikayya gaba kuma wanda zai iya daukar matakan nan take wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke damun sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.