Isa ga babban shafi
Najeriya

Osinbajo ya bada umarnin yi wa rundunar SARS garambawul

Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya bada umurni ga Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da ya yi garambawul ga rundunar yaki da fashi da makamai, wato SARS saboda tarin korafe-korafen da ake yi kan yadda rundunar ke gudanar da ayyukanta.

'Yan Najeriya na zargin rundunar SARS da cin zarafin jama'a
'Yan Najeriya na zargin rundunar SARS da cin zarafin jama'a REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Mai Magana da yawun Osibanjo, Laolu Akande, ya ce saboda korafe-korafen kauce wa tsarin gudanar da aiki da kuma cin zarafin jama’a, ya zama wajibi ga Sufeto Janar da ya yi wa rundunar gyaran fuska da kuma tabbatar da cewar, tana aiki kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Tun a shekarar da ta gabata, aka kaddamar da wani kamfe na ganin an rusa rundunar ta SARS wadda aka kafa tsaboda yaki da gaggan barayi.

Tuni Sufeto Janar na kasar, Ibrahim Idris ya fara aiwatar da umarnin, in da wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan kasar ya fitar, DCP Jimoh Moshood ta ce, daga yanzu an sauya wa rundunar suna daga SARS zuwa FSARS, wato rundunar gwamnatin tarayya ta musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami.

Sanarwar ta kara da cewa, an nada sabon Kwamishinan ‘yan sanda a matsayin shugaban FSARS a duk fadin Najeriya.

bangare guda Osinbajo ya umarci Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta kasar da ta kafa wani kwamitin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa jami’an SRS na cin zarafin ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.