Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga a Borno

Wasu daga cikin jami’an sojin Najeriya da ke cikin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ mai yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar sun yi bore.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. CNBC Africa
Talla

Sojojin wadanda yawansu ya kai kimanin 300, sun yi boren ne a ranar Lahadi a filin jiragen sama da ke garin Maiduguri, in da suka rika harbin iska, abin da ya razana maniyyata aikin Hajjin bana dake shirin tashi.

Majiyar sojojin ta ce, sun yi boren ne domin nuna rashin amincewarsu da shirin tura su karamar hukumar Marte bayan sun kwashe shekaru kusan 4 suna yaki a Barno ba tare da sun yi tozali da iyalansu ba.

Daya daga cikin sojojin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu a Maiduguri cewa, tun a ranar 2 ga watan Fabarairu na shekarar 2015 aka tura su jihar Borno, tare da akalla motoci 55, wadanda ya ce daga cikinsu kwaya uku ne kawai suka rage, sakamakon gwagwarmayar da suka fuskanta, wasu suka lalace yayin da wasu nakiyoyin da aka binne ya tarwatsa su.

A cewar jami’in, babbar bukatarsu ita ce ba su isasshen lokacin hutu domin samun ganawa da iyalansu, da kuma murmurewa don sake samun karsashin komawa fagen daga, to amma hutun da ake ba su baya wuce kwanaki 14.

A cewar sojin abin da ya fusata su shi ne yadda aka nemi a tura su Marte daga tsaron filin jiragen saman Maiduguri, in da za a musanya su da wasu sojin da za a turo daga cikin birnin na Maiduguri.

Sai dai da safiyar ranar Litinin, boren ya zo karshe, bayan da sabon shugaban rundunar ta Operation Lafiya Dole Manjo Janar Abba Dikko ya gana da sojojin da suka fusata.

Cikin sanawar da mataimakin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole ya fitar, Kanar Onyema Nwachukwu, rundunar sojin Najeriyar ta ce, za ta dauki matakan da suka dace wajen ganin ba a sake samun makamanciyar matsalar boren sojin ba.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu la’akari da kawo karshen sabanin da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.