Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba zan sauka daga shugabancin Majalisa ba- Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya,Sanata  Bukola Saraki ya ce, ba zai amsa kiraye-kirayen da wasu ke yi masa na ajiye kujerarsa a Majalisar ba bayan sauya shekarsa daga APC zuwa PDP.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Paul Carsten
Talla

Saraki ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da ya gudana a harabar Majalisar Dattwan a ranar Laraba.

Tun bayan da ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ta PDP ta adawa, Saraki ke ta shan kiraye-kiraye daga bangaren APC don ganin ya sauka daga mukaminsa saboda rashin rinjayen PDP a Majalisar Dattawan.

A cewar Saraki, mambobin Majalisar ne suka zabe shi akan wannan mukami, don haka ba zai saurari duk wani matsin lamba ba.

Shugaban Majalisar ya ce, muddin kashi biyu bisa uku na mambobin Majalisar suka kada kuri’ar yankar kauna a kansa, to babu shakka zai sauka daga kujerar cikin lumana.

Wannan dai na zuwa ne bayan jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta SSS sun datse kofar shiga zauren Majalisar a ranar Talata kafin daga bisa suka bude hanya ga Sanatoci da ‘yan majalisun wakilai, abin da ya haifar da zafafen cece-kuce a fadin kasar har ta kai ga sallamar shugaban hukumar ta SSS, Lawan Daura daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.