Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun datse kofar shiga Majalisar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami’an tsaron farin kaya wato SSS sun datse kofar shiga zauren Majalisar Dokokin kasar, matakin da ake kallo a matsayin wani yunkurin taimaka wa Sanatocin da ke goyon bayan shugaba Buhari tsige shugaban Majalisar, Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

Majalisar Tarayyar Najeriya
Majalisar Tarayyar Najeriya Mashable NG
Talla

An tilasta wa mambobin Majalisar Wakilai da ma’aikatan Majalisar Dattawa komawa bayan sun doshi shiga harabar majalisar kamar yadda rahotanni ke cewa.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, kimanin sanatoci 30 da ke goyon bayan shugaba Buhari sun gudanar da wani taro a cikin daren da ya gabata tare da Darekta Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya ta kasar, Lawan Daura don tattaunawa kan yadda za a tsige Saraki.

Jaridar ta kara da cewa, kwararan majiyoyi sun shaida ma ta cewa, Sanatocin sun shirya nada Ahmed Lawan a matsayin shugaban Majalisar Dattawa don maye gurbin Saraki, yayin da Hope Uzodinma zai kasance mataimakinsa.

A halin yanzu, jami’an ‘yan sanda na ci gaba da tururuwa zuwa zauren Majalisar Tarayyar kasar da ke birnin Abuja.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake sa ran Saraki zai jagoranci wani zama a yau Talata don tattaunawa kan batutuwa da dama ciki har da zaben 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.