Bakonmu a Yau
Alhaji Mamman Abubakar Danmusa kan makomar shugabancin majalisar dattijan Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:39
A Najeriya, yanzu ana ci gaba da yin kira ga shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki, da ya kira zaman majalisar domin komawa a bakin aiki, wanda hakan zai bayar da damar tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi kasar.Wasu dai na ganin cewa daya daga cikin batutuwan da za su iya mamaye zaman majalisar idan aka dawo daga hutu, shi ne makomar mukamin shugabancin majalisar bayan da Saraki ya canza sheka daga APC zuwa PDP.Alhaji Mamman Abubakar Danmusa, tsohon mataimakin shugaban Majalisar dattawan Najeriya a Jamhuriyar ta biyu, ya bayyana mahangarsa dangane da wannan badakala.