Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga a kauyukan Zamfara

Jami’an sojin saman Najeriya, sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga 20, a wani farmaki da suka kai da jiragen yaki biyu, kan kauyukan Yanwari da Mashema da ke jihar Zamfara.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS
Talla

Cikin sanarwar da rundunar sojin saman Najeriya ta fitar a ranar Juma’a, ta ce an samu nasarar ce cikin hadin gwiwarta da sojin kasa, karkashin shirin yakar hare-haren ‘yan bindiga a sassan jihar da sauran ayyukan ta’addanci, wanda aka yi wa lakabi da ‘Operation Dirar Mikiya’

A ranar 31 ga watan Yuli da ya kare, rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da shirin na Operation Dirar Mikiya’ a jihar ta Zamfara, da nufin bankado wuraren da ‘yan bindiga ke boye da kuma murkushe su.

Daraktan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce farmakin zai ci gaba har sai an kawo karshen kashe rayukan jama’a, satar shanu da sauran aukkan ta’asar da ke aukuwa a yankunan da lamarin ya shafa.

Daraktan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce sojin kasa ne suka fara cin karo da ‘yan bindigar wasu haye kan babura, tare da wasu daruruwan shanu da suka sace, daga bisani suka bukaci agajin jiragen yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.