Sauyin shekar wasu 'yan majalisu alheri ne ga jam'iyyar APC - Oshiomhole
Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Adams Oshiomhole ya ce ficewar wasu sanatoci da kuma ‘yan majalisar wakilai daga jami’yyar, nasara ce ga a gare ta, sabanin akasin haka da wasu ke gani.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Oshiomhole ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja, bayan ganawarsa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Sanatoci 15 da kuma ‘yan majalisar wakilai 37 ne suka fice daga cikin jam’iyyar APC, bisa dalilan rashin gamsuwa da ayyuka da kuma manufofin gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari.
Daga cikin wadanda suka yi sauyin shekar, akwai Rabi’u Musa Kwankwaso mai wakiltar Kano ta tsakiya da Dino Melaye mai wakiltar Kogi ta yamma da kuma Suleiman Hunkuyi daga Kaduna ta Arewa.
Shugaban na APC, Adams Oshiomhole ya bayyana wadanda suka fice daga cikin jam’iyyar a matsayin wadanda ba su amince da kyawawan manufofin da ta sa a gaba ba.
A cewar Oshiomhole, abin farin ciki ne ganin yanzu, za a gina jami’yyar APC mai karfi, da ba za ta zama wani tsani na samun mukaman siyasa ko son zuciya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu