Isa ga babban shafi
Najeriya

Fayemi ya lashe zaben kujerar Gwamnan jihar Ekiti

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC dakta John Kayode Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a ranar Asabar 14 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Tsohon ministan bunkasa sarrafa ma'adanai da karafa na Najeriya, Kayode Fayemi da hukumar INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.
Tsohon ministan bunkasa sarrafa ma'adanai da karafa na Najeriya, Kayode Fayemi da hukumar INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti. Reuters
Talla

INEC ta ce Fayemi ya lashe zaben ne, bayan samun jimillar kuri’u dubu 197, 459.

Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Farfesa Kolapo Olusola Eleka ne ya zo a matsayi na biyu, bayan lashe kuri’u dubu 178, 121, sai kuma dan takarar kujerar gwamnan jihar ta Ekiti a karkashin jami’iyyar PDC da ya zo na uku da samun kuri’u dubu 1, 242.

Da safiyar yau Lahadi, 15 ga watan Yuli na shekarar 2018 da muke ciki, shugaban hukumar zaben Najeriya na jihar ta Ekiti, kuma shugaban jami’ar Ibadan, Farfesa Abel Idowu Olayinka ya sanar da sakamakon zaben, wanda 'yan takara 34 suka fafata.

Kafin kada kuri'un dai alkalaumman hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta sun nuna cewa yawan masu kada kuri’ar da ta yi wa rijista ya kai, dubu 913 da 334, sai dai an tantance dubu 667 da 270 ne daga cikinsu, wato kashi 73 na wadanda suka cancanci kada kuri’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.