Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 73 sun hallaka sakamakon rikicin kabilanci a Taraba

Rahotanni daga Taraba da ke tarayyar Najeriya sun ce akalla mutane 73 sun hallaka yayin da aka kone kauyuka da dama, sakamakon barkewar rikicin kabilanci a tsakanin Hausawa, Fulani da sauran kabilu mazauna yankin Yandang da ke karamar hukumar Lau a jihar ta Taraba.

Rkicin kabilanci ya tilastawa mutane masu yawan gaske gudun hijira a jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya.
Rkicin kabilanci ya tilastawa mutane masu yawan gaske gudun hijira a jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya. Daily Trust
Talla

Shugaban kungiyar makiyaya Fulani ta Miyatti Allah na jihar Alhaji Sahabi Mahmoud ya shaidawa manema labarai a garin Jalingo cewa, rikici ya fara ne tun daga ranar 5 ga watan Yuli na shekarar 2018 da muke ciki, kuma akalla Fulani 23 ne suka hallaka.

Shugaban na Miyatti Allah ya ce kusan mutane 10,000 da rikicin ya ke gudun hijira a garin Jalingo, da wasu makwabtan kananan hukumomin jihar ta Taraba.

A nasa bangaren shugaban sauran kabilu da ke zaune a yankin na Yandang Mista Aaron Artimas yace sama da mutanensa 50 ne suka hallaka a rikicin kabilancin.

Yayin da yake yin Allah Wadai da rikicin, Artimas ya jaddada cewa, baki dayan kabilun Hausawa, Fulani, Yandang, Mumuye, Yoti da sauran kabilu, sun kwashe shekaru masu yawan gaske suna zaune cikin kwanciyar hankali tamkar ‘yan uwa, dan haka acewar shugaban, wasu baki ne suka haddasa musu wannan rikici, watakila saboda manufar siyasa.

Tuni dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, David Misal ya tabbatar da aukuwar rikicin sai dai ya ce basu kai ga tantance adadain wadan suka rasa rayukansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.