Isa ga babban shafi

Ziyarar shugaba Emmanuel Macron a Najeriya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari a birnin Abuja
Chanzawa ranar: 05/07/2018 - 20:14

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kammala ziyarar kwanaki biyu a kasashen Afrika, in da halarci taron shugabannin nahiyar da aka gudanar a Mauritania kafin daga bisani ya isa Najeriya don ganawa da takwaransa Muhammadu Buhari. Shugaba Macron ya yi alkawarin tallafa wa Najeriya da sauran kasashen yankin Sahel da kudaden da yawansu ya kai Dalar Amurka miliyan 75 don yaki da ayyukan ta'addanci. Kazalika shugaban ya ce, gwamnatinsa za ta bai wa Najeriya rancen Dala miliyan 475 don inganta harkar sufuri a jihar Legas da samar da ruwan sha a jihar Kano da kuma inganta gandun dajin da ke jihar Ogun. Macron wanda ya ziyarci gidan rawa na Fela da ke birnin Legas, ya jaddada aniyar Faransa ta hada kai da Najeriya wajen bunkasa al'adun nahiyar Afrika.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.